Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Yace rashawar da ake tafkawa a ƙasar ya karu kamar yadda rahotanta ke nunawa cikin shekaru biyu.
Najeriya dai na bin Guinea Bissau wacce ita ce ta ɗaya a ƙasashen da aka fi tafka rashawa a yankin kudu da hamadar saharar Afirka.
Rahoton wanda aka fitar tare da hadin-gwiwar kungiyar da ke fafutukar inganta harkokin majalisun dokoki ta CISLAC ya nuna cewa gwamnatin Najeriya ta samu koma-baya dangane da yadda al`ummar kasar ke kallon yakin da take yi da cin hanci da rashawa.
Rahoton ya kuma nuna yadda annobar korona ya bankado irin wadanan rashawar da gibin da ake dashi a fanin lafiya da yada aka rinƙa handame kuɗaɗen tallafin gaggawa.
Mallam Awwal Musa Rafsanjani, wakilin kungiyar Transparency International a Najeriya ya ce "Cin hanci da rashawa a harkar tsaro ya ja har aka yi zanga-zangar EndSars.
342/